![Muhammadu Buhari](http://arewa.ng/wp-content/uploads/2019/04/Buhari-ya-sa-baki-kan-batun-Zainab-Aliyu.jpg)
Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Shari’a Abubakar Malami da ya shiga maganar Zainab Aliyu, ‘yar Najeriyar nan da ke tsare a kasar Saudiyya.
Jami’an tsaron Saudiyya sun kama Zainab Aliyu ne jim kadan bayan sun isa Saudiyya don yin aikin Umara ita da mahaifiyarta Maryam da kuma ‘yar uwarta Hajara.
Sun zarge ta da safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.
Amma tuni hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewa wasu ma’aikata ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) ne suka saka mata kwayar a jakarta.
Kwamandan hukumar mai kula da MAKIA Ambrose Omorou ya tabbatar wa da BBC cewa tuni suka kama mutum shida, wadanda ake zargi da aikata hakan.
Uku daga cikinsu ma’aikata ne da ke tantance kayayyakin matafiya, daya ma’aikacin wani kamfanin sufurin jirgin sama ne, sauran biyun kuma jmai’an tsaro ne a filin jirgin saman.
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter, Abike Dabiri-Erewa mataimakiya ta musamman ga Shugaba Buhari kan harkokin kasashen waje ta ce shugaban ya umarci Abubakar Malami da ya shiga maganar.
“Buhari ya umarci ministan shari’a da ya yi dukkanin mai yiwuwa don ganin an yi wa Zainab adalci. Mahaifinta ne ya sanar da mu kuma muna samun ci gaba game da ita da sauran mutum biyun,” kamar yadda Abike Dabiri ta bayyana.
Wannan ya biyo bayan maganar da Sanata Shehu Sani ya yi ne, inda yake shawartar iyayen Zainab da su kawo kokensu gaban majalisar dokokin kasar domin ta shiga lamarin.
Dabiri ta kuma shaida wa jaridar Premium Times cewa Buhari ya shiga lamarin a lokacin da ya samu labari mako biyu da suka gabata.