Wata ƙungiyar matasan arewacin Najeriya mai suna Arewa Youth Assembly sun yi kira ga hamshaƙin ɗan kasuwa, wato Alhaji Aliko Dangote, da ya fito takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Matasan ba a nan suka tsaya ba, sun mika kiraye-kirayen nasu har zuwa ga Mr. Femi Otedola da kuma tsohuwar ministar kudin Najeriya Ngozi Okonja-Iweala.
A cewar matasan, sun yi wannan kira ne saboda ganin irin nasarorin da waɗannam mutane ne suka samu a harkar kasuwancinsu.
Don haka ya kamata su zo su gwada sa’arsu don ceto Najeriya daga halin ni-ƴasu da ta shiga a shekarun baya.