Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna inda aka kashe wasu fasinjoji.
An bayyana wanda ya shirya harin da suna Ibrahim Abdullahi, wanda kuma aka fi sani da Mandi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana hakan a Kaduna a ranar Alhamis, ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin yana cikin waɗanda suka sace daliban jami’ar Greenfield a shekarar 2021.
Adejobi ya kuma kara da cewa an kama shi da bindigun AK-47 guda 48, kuma ana ci gaba da kokarin gano wanda ya dauki nauyinsa da kuma sama masa da makamai.