Ƴan ta’adda sun kashe limami da mamu a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar Talata sun kai farmaki wani masallaci da ke unguwar Sabon Layi, unguwar Kakangi a karamar hukumar Birnin-Gwari ta Jihar Kaduna, inda suka kashe limamin da wani mai ibada mai suna Kabir, tare da jikkata wasu biyu.

Wasu masu ibada biyu da suka samu munanan raunuka a harin an bayyana sunayensu Bilya Mairabo da Ashiru Mairabo.

An ce suna jinya a babban asibitin Jibrin Maigwari da ke Birnin-Gwari.

Wani shugaban gargajiya mai suna Zubair AbduRrauf ya bayyana ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5 na safe.

AbduRrauf, wanda ke rike da sarautar Danmasanin Birnin-Gwari, ya kara da cewa a kusan kullum ‘yan bindigar suna kai hari a kauyukan Birnin-Gwari, inda suka yi ta kashe-kashe tare da yin garkuwa da mazauna yankin, musamman manoma.

Ya kara da cewa lamarin ya fi daukar hankali a hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna, kuma ya zama ruwan dare ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar.

Ya ce, “Eh, an kashe limamin masallaci da wasu masu ibada guda biyu. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safiyar ranar Talata. Wasu masallata biyu suna babban asibitin Jibrin Maigwari, Birnin-Gwari.

More from this stream

Recomended