Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta ce ta kama ta ce ta kama wasu sojan gona guda biyu Jonathan Yahaya da Muhammad Umar.
Benjamin Hundeyin mai magana da yawun rundunar shi ne ya bayyana haka a ranar Laraba.
Hundeyin ya ce wani soja mai muƙamin manjo ne dake barikin soja ta shiya ta 81 da ake kira Nigerian Army Provost, Bonny Camp, Victoria Island, Lagos shi ne ya kai mutanen biyu ofishin ƴan sanda na Onikan bayan da aka kama su.
Mai magana da yawun rundunar ya ce sojoji sun kama ɗaya daga cikin mutanen ne sanye da wandon kakin soja da kuma takalmi a yayin da ɗayan kuma aka kama shi sanye da kakin soja.
“Biyo bayan tambayoyi an gano cewa dukkanin mutanen biyu sojan gona ne. Sun gaza faɗar yadda suka mallaki kakin soja shine dalilin kama su.” a cewar Hundeyin.