Ƴan sanda sun kama wani matashi da  ya kashe mahaifinsa a Jos

Rundunar ƴansandan jihar Filato ta kama wani matashi, Joseph Yakubu mai shekaru 29 da ake zargi da kisan mahaifinsa Yakubu Dalyop ta hanyar buga masa taɓarya.

Da yake gabatar da mai laifin a gaban Æ´an jarida a hedkwatar rundunar Æ´an sandan jihar Filato,kwamishinan Æ´an sandan jihar Hassan Steve Yabanet ya ce lamarin ya faru bayan da mahaifin da É—an nasa  suka samu saÉ“ani inda shi kuma ya É—auki taÉ“arya ya buge shi a ka.

Ya ce lamarin da ya faru a ranar 15 ga watan Fabrairu a Kambel dake Anglo-Jos inda wani maƙocinsu ya kai rahoton faruwar haka ofishin ƴan sanda na Anglo-Jos a ranar 20 ga watan Faburairu bayan da mutumin ya mutu a asibitin kwararru na jihar Filato inda yake jiya.

Kwamishinan ya ce an ajiye gawar a É—akin ajiye gawarwaki inda ya ce da zarar an kammala bincike za a tura mai laifin zuwa kotu.

More News

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...

NFF ta naÉ—a Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagle

An naɗa Finidi George a matsayin sabon mai horar da kungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagle. Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF ita ta...

Gwamnan Edo Zai Fara Biyan 70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ga ma'aikatan jihar inda za a riƙa biyan naira dubu 70,000. Gwamnan...

JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar 2024

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta fitar da sakamakon jarrabawar shekarar 2024, watau sakamakon UTME.Sama da mutane miliyan 1.94...