Ƴan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Sokoto

A cigaba da yaƙi da ƴan fashin daji, ɓatagari da kuma rashin tsaro a fadin Najeriya jami’an rundunar ƴan sandan jihar Sokoto  sun samu nasarar kama wasu mutane biyar da ake zargin su da yin garkuwa da mutane akan hanyar Bodinga- Tambuwal.

Mutanen biyar sun faɗa hannun jami’an tsaro ne a ranar 13 ga watan Faburairu  da misalin ƙarfe 08:30 na dare sakamakon bayanan sirri da rundunar ƴan sandan ta samu.

An kama mutanen ɗauke da bindigar AK-47 guda uku da kuma harsashi guda 90.

Mutanen da aka kama sun haɗa da Abdullahi Ali,Aliyu Muhammad Abdullahi Umar, Aliyu Abdullahi da kuma Mohammed Anas dukkaninsu sun amsa cewa suna kan hanyarsu ta zuwa Tambuwal ne domin yin garkuwa da mutane kafin su fada komar jami’an ƴan sandan.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraɗiyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...