Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mai Shari’a Janet Galadima Gimba tare da ƴaƴanta huɗu a jihar Kaduna.
Alƙaliyar tare da ƴaƴanta anyi garkuwa da su ne daga gidansu dake yankin Mahuta a Kaduna ranar 23 ga watan Yuni.
Masu garkuwar da yawansu ya kai 15 sun mamaye gidan mai shari’ar da daddare lokacin da mijinta wanda likita ne yake wurin aiki.
Da take mayar da martani kan lamarin a ranar Laraba Gloria Ballason babbar jami’ar gudanarwar ƙungiyar House Of Justice tayi kira da a bawa alƙaliyar kariya ita da iyalin ta.
Ballason ta ce masu garkuwar sun kashe, Victor Gimba ɗan alƙaliyar mai shekaru 14 a ranar 02 ga watan Yuli.
Kawo yanzu ƴan fashin dajin sun buƙaci a biya su miliyan 300 a matsayin kuɗin fansa inda suka yi alkawarin fara kashe mutanen ɗaya bayan ɗaya matuƙar aka samu jinkirin biyan kuɗin.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna,Mansir Hassan ya tabbatar da faruwar.