Yan bindiga sun sace,Mr. Safiyanu Andaha shugaban karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.
A cewar rahotanni yan bindigar sun sace shugaban karamar hukumar tare da wasu mutane ciki har da wani fitaccen mutum mai taimakon jama’a, Adamu umar wanda aka fi sani da Macciɗo.
Wakilin jaridar Daily Trust ya rawaito cewa shugaban karamar hukumar da sauran mutanen an yi garkuwa da su ne akan titin Andaha-Akwanga da yammacin ranar Litinin.
Wani makusancin shugaban karamar hukumar ya faɗawa jaridar cewa yan bindigar sun fito ne daga cikin daji suka kuma awon gaba da mutanen ya zuwa wani guri da ba asan ko ina ne ba.
Har ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoton rundunar yan sandan jihar Nasarawa bata fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin.