Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau

An sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ba a tantance adadinsu ba da sanyin safiyar Juma’a.

‘Yan ta’addan masu yawan gaske sun mamaye al’ummar Sabon-Gida da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Wani mazaunin unguwar Sabon-Gida mai suna Nazeer Sabon-Gida ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar garin ne da misalin karfe uku na safe inda suka fara harbe-harbe ba gaira ba dalili.

A cewarsa, an kai hari a dakunan kwanan dalibai uku, kuma ‘yan bindigar sun tafi da dukkan daliban da ke cikin dakunan kwanan dalibai.

“Sun shiga garin da misalin karfe 3 na safe kuma suka fara harbi ba kakkautawa,” in ji shi.

“Har yanzu ba mu tabbatar da adadin daliban da aka yi garkuwa da su ba saboda ‘yan bindigar sun shiga dakunan kwanan dalibai uku tare da yin garkuwa da dukkan daliban da ke wurin. Yana da wahala a iya tantance adadinsu a yanzu.”

More from this stream

Recomended