Akalla mutane 29 ne aka kashe a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Runji da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Harin wanda ya faru da misalin karfe 10 na daren ranar Asabar na zuwa ne kwanaki uku bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane takwas a kauyen Atak’Njei da ke karamar hukumar Zangon Kataf.
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan wanda ya tabbatar da faruwar sabon lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an kona gidaje da dama a cikin al’ummar yankin yayin da wasu maharan suka jikkata.
Ya kuma bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun yi mumunar arangama da ‘yan bindigar kuma suna nan a yankin gaba daya domin tabbatar da doka da oda.