Ƙungiyar ƙwadago ta caccaki gwamnati kan tallafin naira biliyan biya-biyar ga jihohi

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta caccaki gwamnatin tarayya a kan tallafin da ta bayar wa jihohi bayan cire tallafin man fetur.

Idan ba manta ba, Gwamnatin Tarayya a watanni baya ta cire tallafin man fetur, ta kuma baiwa gwamnatocin jihohi tallafin abinci don ci gaba da rabawa ‘yan Najeriya tare da Naira biliyan 5.

Sai dai sa’o’i bayan ayyana yajin aikin kwanaki biyu a fadin kasar sakamakon illolin cire tallafin man fetur, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce rabon kayan abinci bai wadatar ba wajen yaki da illar matakin da gwamnati ta dauka.

“Idan kun raba wannan N5bn ko ma manyan motoci biyar na shinkafa ko hatsi, mutane da yawa ba za su samu kofin shinkafa daya ko rabin ba,” in ji shi.

“Idan ka raba N5bn, mutane da yawa, watakila a cikin ma’aikata ko talakawa, ba za su samu N1,500 ba. Yanzu, wannan shi ne tallafin?”

More News

Gwamnatin Adamawa Ta Ƙara Hutun Ɗaliban Makarantu Saboda Annobar Cutar Ƙyanda

Gwamnatin jihar Adamawa ta tsawaita lokacin komawar ɗaliban jihar makarantunsu domin fara  zangon karatu na uku saboda annobar cutar ƙyanda. A wata sanarwa ranar Litinin,...

Sojan Jamhuriyar Nijar sun kama Gawurtaccen Ɗan Fashin dajin Najeriya Kachalla Mai Daji

Dakarun sojan Jamhuriyar Nijar sun samu nasara kama gawurtaccen ɗan fashin dajin nan mai suna Kachalla Mai Daji a garin Illela dake kan iyakar...

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraɗiyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...