Ɗalibar aji huɗu a jami’a ta kashe kanta saboda rashin ƙoƙari a makaranta

Wata daliba mai ƴar aji huɗu a jami’ar jihar Kwara, Malete da ke karamar hukumar Moro, mai suna Rashidat Shittu, ta kashe kanta saboda yanayin ƙoƙarinta a karatu.

A cewar abokan karatunta da suka bayyana cewa marigayiyar ta kashe kanta ne gabanin jarrabawar da ta ke tafe ta hanyar shan maganin ƙwari.

An ce Shittu ta mutu ne a lokacin da ta isa asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin inda aka garzaya da ita domin yi mata magani.

An ruwaito cewa an fara kai ta asibitin makaranta ne kafin daga bisani a kai ta asibitin koyarwa domin ceto rayuwarta.

Har ila yau, wata ma’aikaciyar da ke cikin tawagar likitocin da suka je wurinta a UITH amma ba ta son a bayyana sunanta ta ce a mace aka kawo dalibar.

More from this stream

Recomended