Ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargi da kashe ɗan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane uku da ake zargi da kashe wani dan sanda mai suna Bala Magaji a ranar 25 ga Yuli, 2023.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya ba wa manema labarai ranar Laraba.

Ya ce an kashe Magaji, dan sandan da ke aiki a hedikwatar ‘yan sanda ta Darazo a lokacin da yake bakin aiki a Anguwar Abuja a kauyen Konkiyel.

Mista Wakili ytce, “Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu wajen kisan wani dan sanda a kauyen Konkiyel da ke karamar hukumar Darazo a jihar.

“An kai harin ne a ranar 25 ga Yuli, 2023, kan dan sanda Bala Magaji wanda ke aiki a hedikwatar ‘yan sanda ta Darazo, yayin da yake bakin aiki a Anguwar Abuja a kauyen Konkiyel.

More News

Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...