Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da suka yi bacci a lokacin da suke tsare da mutanen da suka sace

Jami’an ƴan sanda sun samu nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane bayan da suka buge da sharar bacci a lokacin da suke tsare da wasu mutane da suka sace.

An kama mutanen a yankin Ofosu dake jihar Ondo a lokacin da suka yi garkuwa da  matar wani fasto da kuma wasu mutane biyu.

Oladunlami  Ibukun mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ondo shi ne tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar lamarin.

A cewar Ibukun mutanen da suka kuɓuta sun bayyana cewa sun tsere ne bayan da waɗanda suke tsare da su suka fara sharar bacci sakamakon ƙwayoyin maye  da suka sha.

“Mutanen ba a lokaci ɗaya suka kuɓuta ba,” a cewar mai magana da yawun rundunar.

Masu garkuwar da aka kama sun haɗa da Garba Mumini mai shekaru 27, Yusuf Tale shekaru 21, Kabiru Muhammad mau mai shekaru 16, Shaibu Umaru da Adamu Muhammad.

Ibukun ya ƙara da cewa masu garkuwar sun tsere daga jihar bayan da suka yi garkuwar a watan da ya wuce amma an kama musu bayan da ɗaya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ya gane ɗaya daga cikinsu.

More from this stream

Recomended