Ƴan sanda a Jigawa sun yi babban kamu yayin da suka damƙe masu garkuwa da mutane

Ƴan sanda a jihar Jigawa sun kama wasu mutane hudu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma wani mai kera makamai.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Shiisu Adam, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa an kama mutanen ne ta hanyar hadin gwiwa da jami’an ‘yan sanda da ’yan banga na yankin suka yi.

A cewar Adam, yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin kerawa da kuma sayar da bindigogi ga wasu da ba a riga an tantance su ba.

More from this stream

Recomended