‘Yan makaranta 137 da aka sace daga Kuriga, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, wadanda aka sako ranar Lahadi, sun isa gidan gwamnati da ke Kaduna.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sakin yaran.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun gwamnan jihar Uba Sani.