Bakwai daga cikin yan majalisar dokokin jihar Zamfara 24 sun dakatar da yan majalisar jihar su 16 da ake zargin sun yi yunkurin tsige kakakin majalisar dokokin jihar,Bilyaminu Moriki.
A ranar Juma’a ne mambobin majalisar su 16 suka sanar da matsayar da suka dauka ta dakatar da Moriki saboda tsawon lokacin da ya ɗauka baya jihar duk da cewa jihar na fama da hare-haren ƴan fashin daji.
Dakatarwar ta biyo bayan kuɗirin da Nasiru Abdullahi mamba mai wakiltar mazaɓar Maru ya gabatar.
Mambobin sun kuma naɗa Bashar Gummi a matsayin kakakin majalisar na riƙo.
A yayin zaman majalisar na ranar Litinin majalisar ƙarƙashin jagoranci Moriki ta ayyana zaman da waɗancan ƴan majalisar dokokin suka yi a matsayin haramtacce.
Sun yi kira ga mutanen jihar da su yi watsi da labaran da ake yaɗawa na dakatar da shugaban majalisar.
Ƴan majalisar sun yi zargin cewa wasu manyan ƴan siyasa dake zaune a wajen jihar su ne ke ɗaukar nauyin abokan aikinsu domin su kawo tangarɗa ga gwamnatin,Dauda Lawal Dare.