Kungiyar kwadago ta ce za ta gudanar da zanga-zangar da ta shirya yi a fadin kasar ranar Laraba duk da bayani game da shirin cire tallafin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wani jawabi inda ya ce an ware N500bn ga masana’antu, kananan ‘yan kasuwa da manoma. Ya kuma fitar da shirye-shiryen kara albashi da kuma sayen manyan motocin bas guda 3,000.
Duk da yunkurin da shugaban kasar ya yi na dakile zanga-zangar ƴa kwadagon, shugaban kungiyar ta Najeriya, Joe Ajaero, ya ce ba za su fasa zanga-zangar ba.
Ajaero ya yi magana ne jim kadan bayan tattaunawa tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya a ranar Litinin din da ta gabata, inda ba a cimma matsaya ba. Ana sa ran za a ci gaba da tattaunawa ranar Talata (yau).