Jami’an rundunar ‘yan sanda na helkwatar reshen Okokomaiko, a ranar Asabar, sun kama wasu mutane biyu bayan da suka tare wata motar bas ta Volkswagen LT a unguwar Afromedia da ake zargin suna dauke da wasu katan-katan na muggan kwayoyi.
Rahotanni sun nuna cewa kwali 70 na Feed Fine Cyproheptadine Caplets 4gnaka kama a cikin motar.
An tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya fitar a shafinsa na X ranar Lahadi.
Sanarwar ta tabbatar da cewa mutanen biyu da ke cikin motar, Augustine Egemoye mai shekaru 60 da Innocent Eremosele, mai shekaru 35, sun amsa laifinsu tare da bayyana cewa suna kai wa wani a Alaba maganin ne, wanda zai buga sabuwar ranar lalacewa sannan kuma a ci gaba da sayarwa.