Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin da daddare a ƙofar gidansa dake Ilukpa, Iyara inda ƴan bindigar suka riƙa harbi sai kace sojoji a filin daga kafin su yi awon gaba da shi.
Mr E.K Adebayo jami’in hulda da jama’a na Kungiyar Cigaban Iyara ya bayyana rashin dacewar yin garkuwa da limamin musamman a wannan lokacin na watan Azumin Ramadan.
Ya yi kira ga hukumomin da suka da ce da su tabbatar an sako malamin addinin.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kogi, William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin.