
Aƙalla mutane 4 ne suka mutu a wani hari da aka kai wani ginin jami’an hukumar lura da shige da fice ta Najeriya biya bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai musu a jihar Kebbi..
A wata sanarwa ranar Talata, Kenneth Udo mai magana da yawun hukumar ya ce an kai harin ne ranar Juma’a a ƙaramar hukumar Kangiwa ta jihar..
Udo ya ce an kashe mai gadi guda ɗaya sai kuma wasu ƴan kwangila su uku inda ya ƙara da cewa babu ma’aikacin hukumar ko ƙwaya ɗaya da ya mutu a harin.
“Hukumar na alhinin sanar da harin baya bayannan da ake zargin ƴan bindiga da kai wa kan wani dake kan iyaka da kuma wasu ƴan kwangila dake aiki a wurin akan bodar Kangiwa dake ƙaramar hukumar Kangiwa ta jihar Kebbi da karfe 07:20 na daren ranar Juma’a 10 ga watan Janairu 2025,” sanarwar ta ce..
Sanarwar ta kara da cewa rundunar na cigaba da aiki da sauran hukumomin tsaro domin gano maharan.