Ƴan Bindiga Sun Kashe Ɗan Sanda Ɗaya Tare  Kubutar Ɗaurarru  7 Daga Wani Gidan Yari A Jihar Imo

Aƙalla  ɗaurarru 7 dake gidan yarin Okigwe a jihar Imo suka tsere daga gidan yari a wani hari da ƴan bindiga suka kai a ranar Litinin.

A wata sanarwa da aka fitar bayan kai harin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,Henry Okoye ya ce maharan sun kuma kashe insifectan ɗan sanda.

Okoye ya ce kwamishinan yan sandan jihar,Aboki Danjuma ya tura rundunar kar ta kwana da za ta bi sawun maharan.

Ya ƙara da cewa ana zargin yan bindigar mambobi ne na ƙungiyar ƴan ta’addar IPOB dake fafutukar kafa ƙasar Biafra.

Jihar Imo dai ta kasance jihar dake gaba-gaba a yankin kudu maso gabas dake fama da tashin hankalin mayaƙan ƙungiyar ta IPOB.

More from this stream

Recomended