Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci a Garin Shanawa Da Ke Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya na cewa, wasu ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki a masallacin garin Shanawa da ke jihar a daren jiya.

Harin ya faru ne a lokacin da ake gudanar da sallar isha’i, inda ƴan bindigan suka harbi aƙalla mutum huɗu kuma suka yi awon gaba da wasu, tare da ci gaba da ɓoyewa, har zuwa yanzu ba a san adadin su ba.

Bugu da ƙari, rahotanni sun tabbatar da cewa Turji, wanda aka saba jin labarinsa a yankin, ya kai hari a garin Shinkafi a rana ɗaya, inda ya ƙara kwasar ƙarin wasu mutane masu yawa.

More from this stream

Recomended