
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Laraba, ya ziyarci wasu gonaki 10 dake kananan hukumomin hudu a wajen birnin Maiduguri.
Kananan hukumomin sun hada da Maiduguri Metropolitan Council, Mafa, Jere da kumma Difa.
A yayin ziyarar ta bazata Zulum wanda farfesa ne a harkar noman rani ya tattauna da manoman inda ya tambaye su matsaloloin da suke fuskanta domin magance su.
Yawancin gonakin da gwamnan ya ziyarta ya iske manomansu suna nome ciyawa.
Zulum ya yiwa manoman bayani cewa ba kamar sauran jihohi ba jihar Borno bata iya sawo taki ba domin rabawa manoma saboda hani da aka yi daga ofishin mai bada shawara akan harkar tsaro duba da yadda yan taadda ke amfani da shi wajen hada bama-bamai.
Saboda hanin da aka yi zabin da ya rage musu kawai shi ne yin am amfani da taki na ruwa.