Zulum ya yi wa ma’aikatan lafiya a Borno ƙarin albashi mai tsoka

Gwamna Babagana Umar Zulum na jihar Borno ya ce ma’aikatan lafiya da suka amince su yi aiki a karkara za su samu karin kashi 30 cikin 100 na albashin da suke karba a yanzu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da rabon tallafin N100,000 da kayan abinci ga tsofaffi (shekaru 65 zuwa sama) a karkashin kungiyar Renewed Hope Initiative na uwargidan shugaban kasar, Oluremi Tinubu.

Ya ce matakin kuma na daga cikin shirin gwamnatinsa na tallafa wa tsofaffi ta kowace hanya, inda ya ce jihar za ta samar da likitocin da suka kware wajen kula da tsofaffi a cibiyoyin kiwon lafiya a fadin jihar.

Zulum, wanda ya samu wakilcin kwamishinan lafiya, Farfesa Baba Malam Gana, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a kafa sashen kula da tsofaffi a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Borno da ke Maiduguri.

More from this stream

Recomended