Zulum Ya Hana Yin Sana’ar Gwangwan a Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya hana sana’ar baban bola ko kuma yan gwangwan a dukkanin kananan hukumomin jihar 27.

Gwamnan ya sanar da hanin ne a kokarin dakile cigaba da kashe yan gwangwan da mayakan Boko Haram suke cigaba da yi musamman a wajen wasu wasu kananan hukumomi da kuma dakatar da satar kayan jama’a da na gwamnati.

Da yake sanar da hanin ranar Litinin, gwamna Zulum ya ce ” a cikin shekaru biyar da suka wuce an kashe mutane da dama saboda yin gwangwan hakan ya sa gwamnatin jihar Borno binciken munanan ayyukan.”

“Kun ga dai wannan wurin dukkanin wadannan kayan gwamnati ne bayan ku kuma kayayyaki ne mallakin kamfanonin sadarwa. Wannan ayyuka za a iya cewa zagon kasa ne ga tattalin arzikin gwamnatin tarayya da ta jiha. Saboda haka na bada umarnin hana sana’ar gwangwan a dukkanin kananan hukumomi 27 har zuwa wani lokaci anan gaba. “

Zulum ya kara da cewa masu sana’ar ta gwangwan sun yi fice wajen lalata kayayyakin gwamnati da kuma na jama’a musamman a kananan hukumomin da ayyukan mayakan Boko Haram suka tilastawa jama’a barin gidajensu.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta rasa kayayyaki masu daraja na biliyoyin Naira a cikin shekaru biyar saboda ayyukan yan gwangwan.

More from this stream

Recomended