Zargin ta’addanci: Saudiyya ta zartar wa mutum 37 hukuncin kisa

A man walks beside the Saudi flag in Jeddah, Saudi Arabia, 9 December 2015

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Saudiyya ta zartar wa ‘yan kasar 37 hukuncin kisa bisa zargin ayyukan ta’addanci a ranar Talata.

An zartar da hukuncin ne kwanaki hudu bayan kashe wasu ‘yan kungiyar IS guda hudu lokacin da suke kokarin kai wa wani ginin jami’an tsaro hari a Riyadh, babban birnin kasar.

Wannan shi ne adadi mafi yawa na mutanen da aka kashe a lokaci guda a Saudiyya cikin shekaru uku.

An aiwatar da hukuncin kisan ne a sassa daban-daban na kasar, ciki har da lardunan da ke gabashinta, inda aka rika samun bore na ‘yan shi’a ‘yan tsiraru, daga lokaci zuwa lokaci.

Cikin yankunan da aka aiwatar da hukuncin har da Makkah da Madina da kuma Riyadh.

Daga cikin wadanda aka zartar wa da hukuncin kisan akwai wadanda suka fito daga wasu fitattun gidaje da ma kabilu a Saudiyyar.

An same su ne da laifin rungumar akidar tsaurin ra’ayi, da kafa kungiyoyi na ‘yan ta’adda da kai hare-haren da suka haddasa mutuwar dakarun tsaro na kasar.

Daga cikin wadanda aka kashen, akwai wanda aka fille wa kai, daga nan aka gicciye shi jikin wani katako aka bar gawarsa na tsawon sa’o’i domin kowa ya gani.

Saudiyyar dai ta murkushe wata babbar barazana ta kungiyar al-Qaeda sama da 10 da suka wuce, amma duk da haka tuni kungiyar IS ta kafa wani dan karamin reshenta a masarautar.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce Saudiyyar ta yanke wa mutum 149 hukuncin kisa a bara.

Yawanci ana aiwatar da hukuncin kisa ne ta hanyar fille kai. Sannan kuma a kan gicciye mutum ne bayan an kashe shi kan laifukan da hukumomi ke ganin sun fi muni.

A shekarar 2018, an kashe wani mutum aka kuma gicciye shi bayan da aka zarge shi da caka wa wata mata wuka.

An kuma zarge shi da kokarin kashe wani mutumin da suka yi kokarin yi wa wata fyade tare, kamar yadda jaridar Bloomberg ta ruwaito.

Gwamnatin Saudiyya ba ta fitar da wani kiyasi a hukumance ba kan yawan kashe-kashen da ta aiwatar, sai dai kafafen yada labaran kasar na yawan ruwaito labaran hukuncin kisan da ake yi wa mutane.

A ranar Lahadi, Saudiyya ta yi ikirarin dakile wani hari da aka yi niyyar kai wa wata cibiyar tsaro da ke al-Zulfi, a arewacin Riyadh.

An kashe maharan hudu, kamar yadda mai magana da yawun Ofishin Tsaro na Fadar shugaban kasa ya fada.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...