Zanga-zangar SARS: Shugaba Buhari ya gana da tsoffin shugabannin Najeriya

Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi wani taro ta intanet da dukkan tsofaffin shugabanin kasar a jiya Juma’a.

Shugabannin sun hada da Cif Olusegun Obasanjo da Janar Yakubu Gowon da Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Cif Ernest Shonekan da kuma Goodluck Ebele Jonathan.

Shugabannin sun tattauna halin da kasar ke ciki, sakamakon zanga-zangar kyamar rundunar yan sandan SARS, wadda ta rikide zuwa rikici.

Mai ba da shawara na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari kan yada labarai, Malan Garba Shehu ya ce tsohon shugaba Yakubu Gowon da kuma shugaban mai ci ne su ka yanke shawarar kiran taron shugabannin don nemo hanyoyin warware matsalolin da a ke ciki a kasar.

A cewar Garba Shehu tsofaffin shugabannin ‘sun ce sun gamsu da irin muhimman kalaman da ya yi a cikin jawabin nasa, musamman da ya amince cewa zanga zangar lumana abu ne da kundin tsarin mulki ya aminta a yi.’

‘Kuma sun gamsu cewa gwamnati ta amince da bukatun masu zanga zangar lumana kuma an fara aiki kan su.’

To amma Malan Garba Shehu ya ce ‘tsoffin shugabannin sun yi allah-wadai da kwace wannan tarzoma da yan ta’adda su ka yi.

‘Kuma fitinannun mutane suka zo suna kone-kone, suna sata, suna sakin yan fursuna da sauran irin wadannan abubuwa.’

Mai ba wa shugaban Najeriyar shawara ya kara da cewa taron ya tattauna asarar rayuka da dukiyoyi da a ka tabka sanadiyyar rikicin.

A cewarsa an kona gidaje da shaguna 205 kuma mutun 51 sun rasa rayukan su da su ka hada da jami’an tsaro 18.

Dangane da batun kisan masu zangza zangar a jihar Legas, Garba Shehu ya ce ‘ita gwamnatin Legas ta ce za ta daukin nauyin bincike kan abinda ya faru kuma kawo yanzu ba ta kawo cikakken bayanin abun da ya faru a can ba.’

‘Amma su sojoji sun nuna cewa ba ma su je wurin ba ballantana a ce sun yi harbi.’

(BBC Hausa)

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

ÆŠan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...