Zanga-zangar kisan bakar fata ta tsananta a Amurka

Masu zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto
EPA

Ana ci gaba da zanga-zanga a kan kisan da aka yi wa wani bakar fata a Amurka George Floyds.

Wani dan sanda ne ake zargin ya kashe mutumin bayan ya tsare shi a Minneapolis a ranar 25 ga watan Mayun 2020, abin da ya harzuka ‘yan kasar har suke zanga-zanga don neman ayi masa adalci a kan kisan da aka yi masa.

Tuni dai masu zanga-zangar suka yi biris da dokar takaita zirga-zirgar da aka sanya a manyan biranen kasar saboda dakatar da zanga-zangar.

Masu zanga-zangar dai sun ci gaba da zanga-zangar duk da dokar takaita zirga-zirgar da aka sanya a kusan biranen kasar musamman a inda zanga-zangar ta fi tsananta.

A bangare guda kuma wasu masu zanga-zangar sun hadu a garin Floyd wato Texas inda suka hadu tare da iyalansa su ka ci gaba da zanga-zanga.

A Washington DC kuwa, kimanin sojoji 1,600 aka tura domin kwantar da zanga-zangar.

Mahaifiyar ‘yar George Floyd, ta shaida wa wani taron manema labarai cewa a yanzu an mayar da ‘yarta marainiya., kuma mahaifin ‘yarta ta ba zai ga girman ‘yarsa ba, wannan babbar damuwa ce inji ta.

Matar ta ce ba bu abin da take bukata a yanzu illa a yi masa adalci a bi masa hakkinsa saboda shi mutum ne mai kirki bashi da wani mugun hali inji ta.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A wasu biranen Amurka dai jami’an ‘yan sanda da sojoji na tsugunnawa tare da masu zanga-zanga a wani mataki na hadin kai.

A Los Angeles dai masu zanga-zangar na shaida wa jami’an tsaro cewa su shiga cikinsu suyi zanga-zangar tare amma kuma sai su shaida musu cewa a’a su akwai bukatar su tsaya a gefe.

Tuni dai wasu mawaka a kasar suka fara sadaukar da waka ga George Floyd.

A bangare guda kuwa, ana gudanar da irin wannan zanga-zangar a wasu biranin kasar Faransa ciki har da Paris inda masu zanga-zangar ke yi saboda kisan Mr Floyd wanda suka ce an taba makamancin kisan a kasar a shekarar 2016 .

Kusan mutum dubu 20 new suka yi watsi da dokar kullen da aka sanya a kasar saboda cutar korona inda suka fantsama tituna daga baya ma sai suka suka jefa duwatsu inda ‘yan sanda suka mayar musu da martani ta hanyar watsa musu barkwanon tsohuwa.

Kazalika akwai wasu masu zanga-zangar da suka hadu a Liverpool inda suma ke zangaz-zangar amma ta lumana duk a kan kisan George Floyd.

Ba a wadannan birane zanga-zangar ta tsaya ba, ta fanstama wasu kasashen inda suke nuna goyon bayansu suma a kan yi wa Mr Floyd adalci.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...