Wasu matasa sun fantsama kan tituna inda suke zanga-zanga kan tsananin matsin rayuwa da ake fama da shi a ƙasarnan.
Zanga-zangar ta su na zuwa ne kwanaki biyu gabanin fara zanga-zangar da aka shirya farawa a ranar 1 ga watan Agusta.
Amma kuma wasu matasa a garin Suleja dake jihar Niger sun yi riga malam masallaci inda suka fantsama kan tituna ɗauke da kwalaye da aka rubuta “Dole a dawo da tallafin mai” ” Ya isa haka ya isa haka” ” Mu ba bayi bane ƙasarmu” da sauran rubututtuka makamantan haka.
Masu zanga-zangar na jerin gwano ne akan babbar hanyar Abuja-Kaduna ta ratsa garin na Suleja inda suke faɗin kalaman nuna ƙin jinin gwamnati.
Gwamnonin jihohi da kuma shugaban ƙasa sun yi kiraye-kiraye ga matasa da su janye batun zanga-zangar da suke shirin gudanarwa.
Suma jami’an tsaro sun gargadi masu shirya-shirya zanga-zangar cewa wasu ɓata gari ka iya amfani da damar wajen tayar da zaune tsaye.