Zan Kawo Sauyi A Jihar Filato – Simon Lalong

Bayan rantsuwar kama aiki da gwamnan jahar Filato Simon Lalong ya yi na ci gaba da shugabancin jihar karo na biyu, wasu al’ummar jihar sun bayyana fatar samun sauyi masu inganci da zasu kyautata rayuwar su.

Babban batu da yafi dauke hankalin mutane Filato shine batun baiwa matsa aiki yi domin dogaro da kai. Sai batun batun ilimi da inganta karatu ta yanda matasa ba zasu dogara da ayyukan gwamnati ba, su iya kafa sana’o’i domin taimakawa kawunan su kuma hakan zai sa a samu saukin tashe tashen hankula a jihar.

Shiko gwamnan jihar Filato, a hira sa da Muryar Amurka a kwanakin baya, ya yi bayani a kan abubuwan da zai fuskanta a mulkin sa karo na biyu, da suka hada da biyan albashin ma’aikata da samar da tsaro ga al’ummar jihar.

Shima gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar wanda ma’abucin jihar Pilato ne yace yana da yakinin Simon Lalong zai samar da sauye-sauye masu inganci a jahar.

More News

Gwamnatin Enugu ta bayyana dalilin sanya haraji kan gawar mutane

Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin...

ÆŠan tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi ya rasu a hatsarin mota

Faisal Makarfi dan gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi ya rasu. Faisal ya rasu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar...

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...