Babban batu da yafi dauke hankalin mutane Filato shine batun baiwa matsa aiki yi domin dogaro da kai. Sai batun batun ilimi da inganta karatu ta yanda matasa ba zasu dogara da ayyukan gwamnati ba, su iya kafa sana’o’i domin taimakawa kawunan su kuma hakan zai sa a samu saukin tashe tashen hankula a jihar.
Shiko gwamnan jihar Filato, a hira sa da Muryar Amurka a kwanakin baya, ya yi bayani a kan abubuwan da zai fuskanta a mulkin sa karo na biyu, da suka hada da biyan albashin ma’aikata da samar da tsaro ga al’ummar jihar.
Shima gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar wanda ma’abucin jihar Pilato ne yace yana da yakinin Simon Lalong zai samar da sauye-sauye masu inganci a jahar.