Zamfara Ta Zama Cibiyar Ƴan Fashin Daji Muna Buƙatar Ƙarin Sojoji- Dauda Lawal

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya ce a yanzu jihar Zamfara ta zama cibiyar ƴan fashin daji a faɗin arewacin Najeriya.

Lawal ya bayyana haka ne lokacin da yake magana da ƴan jaridun dake fadar shugaban ƙasa bayan da ya yi wata ganawa da shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu.

Ya ce ƙaruwar rashin tsaro da ake samu a jiharsa zai iya mamaye arewacin Najeriya idan ba ayi gaggawar ɗaukar mataki ba.

“An kai farmaki da dama a wasu garuruwa dake ƙananan hukumomin. Inaji cewa a matsayina na gwamnan wanda yasan me yake ya kamata na sanar da shugaban ƙasa halin da ake ciki,” ya ce.

“Zamfara ta zama cibiyar fashin daji a yanzu da muke magana kuma idan ba ayi wani abu akan Zamfara ba bana jin zamu iya warware halin da ake ciki a dukkanin faɗin arewacin Najeriya,”

Ya ce shugaban ƙasa yaji ɗaɗin ganawar ta su kuma za a tura ƙarin sojoji jihar da kuma kayan aikin su.

Lawan ya kuma tabbatar da cewa ɗaliban Kuriga da aka sace a Kaduna a jihar Zamfara aka kubutar da su.

More from this stream

Recomended