Zamfara: Kotu ta sa Matawalle ya mayar da motoci 50 da ya tafi da su bayan ya bar gwamna

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Sokoto ta umarci tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da ya dawo da duk motocin da ke hannunsa.

Umurnin ya ce shi da mataimakinsa su mayar da duk motocin da ake zargin sun tafi da su.

Bayan kin mayar da motocin 50 da Matawalle ya yi, gwamnatin jihar ta yi amfani da umarnin kotu na kwato kadarori.

Sai dai bayan an kwato motocin, Matawalle ya ja maganar zuwa babbar kotun tarayya da ke Gusau.

Daga nan ne kotun ta ba da umarnin a mayar masa da motocin.

More from this stream

Recomended