Zakzaky ya gargadi Tinubu game da kai hari Jamhuriyar Nijar

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan kai wa Jamhuriyar Nijar hari.

El-Zakzaky ya yi zargin cewa Faransa da Amurka, na kokarin amfani da Najeriya wajen kai wa Jamhuriyar Nijar hari.

Ya ce kamata ya yi Tinubu ya fahimci cewa Nijeriya da Jamhuriyar Nijar abu daya ne idan aka duba tarihi, yana mai cewa irin wannan matakin abin mamaki ne.

Ya jaddada cewa kamata ya yi Tinubu ya sake duba shirin kai hari a Jamhuriyar Nijar.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, El-Zakzaky ya gano hadin kan da ke tsakanin Najeriya da Nijar a tarihi.

A cewarsa: “Ba zato ba tsammani, Faransa da Amurka suna so su yi amfani da Najeriya su kai wa Nijar hari.

“Wannan abu ne mai ban mamaki idan aka yi la’akari da cewa Najeriya da Nijar mutane daya ne.

“Masarautu ne aka aka sassaka don haifar da Nijar da Najeriya.”

A ranar Talata ne gwamnatin Nijar ta ki amincewa da sabuwar tawagar diflomasiyya daga kasashen Afirka.

More from this stream

Recomended