Zaben neman aure a Giade shirme ne – Uban yaron da ya ci zabe

[ad_1]

Masu zaben neman auren budurwa a garin Giade na jihar Bauchi


An kada kuri’a 542 yayin zabe tsakainin samari biyun da ke yin takarar

Iyayen saurayin da ya yi nasara a zaben fidda gwani tsakanin ‘yan takarar neman wata budurwa a jihar Bauchi sun yi watsi da abin a matsayin “shirme”.

Labarin yadda mutane suka jefa kuri’ar raba gardamar a garin Giade na jihar Bauchi da ke Arewa maso gabashin Najeriya ya karade kafafen intanet a makon nan.

Kafafen sun ruwaito yadda wata budurwa ta bukaci mutanen gari su yi alkalanci tsakanin samarinta biyu da ta ce tana son su dauka kuma tana gudun a zarge ta da yaudara.

Bayan hakan ne aka tsara gudanar da zaben ‘yar tinke har ma da kotun sauraren kararrakin zabe, yayin da samarin biyu suka yi ta karade garin suna neman goyon bayan jama’a a zaben.

Baturen zaben, Umar Saleh ya ce wanda ya ci zaben ya samu nasara da kuri’a 331 a zaben ‘yar tinken, inda ya bai wa abokin karawarsa mai kuri’a 211 ratar kuri’a 10..

Gaskiyar magana

Malam Danladi Ibrahim, kawun saurayin da ya yi nasara a zaben, ya bayyana wa BBC cewar wasa ne tsakanin yara amma aka yi ta yadawa a shafukan zumunta.

Danladi ya ce shi kansa labarin maganar ya ji a wurin wasu, sannan ya tambaya aka yi masa bayani cewa maganar yara ce.

“To da aka fada mani haka sai aka ce ai irin wasan nan ne na yaran, shi ne har aka dora shi a kan Facebook da Whatsapp.”

Ya ce yaron bai wuci shekara 16 da haihuwa ba, bai isa aure ba sannan ba shi da masaniyar cewa yaron na da wata budurwa.

“To wannan dai shi ne gaskiyar maganar abin da na fada maka: shiririta ce da ma irin ta yara, suka je suka yi ta.

“Ni kaina wallahi da aka kira ni jiya aka fada mani kusan kwana na yi ban yi barci ba, ban rintsa ba, abin ya dame ni.”

Ya ce shi bai taba sanin cewa yaron na da budurwa ba kuma budurwar da ake magana a kanta ba ita ce aka sanya hotonta tare da yaron ba.

“Ita wannan ‘yata ce, ita wannan din da ka gani yayarsa ce ma.”

Yadda abin ya faru

Umar Saleh mai shekara 26, wanda shi ne baturen zaben, ya ce samarin abokai ne da ke gardama a kan wane ne saurayin yarinyar da ake magana a tsakaninsu.

Umar ya ce duk sanda ta zo wucewa sai kowannensu ya rika cewa budurwarsa ce, har dayansu ya nemi su je ta zabi wanda take so, in ya so sai daya ya hakura.

“Dayan ya ce a’a idan muka je ta tantance duk wanda ta ki zaba zai kullace ta. Yanzu sai dai mu yi kuri’a tsakaninmu.

“Duk wanda ya fi mutane a cikin yaran unguwar nan to shi ne mai ita. Sai suka yi yarjejeniya a tsakaninsu kuma kowa ya yarda da hakan.

“Shi ne suka sa kwanakin zaben sannan suka je suka yi ta kamfe suna yada manufarsu.

“Da ranar ta zo mun zata abin nasu wasa ne amma daga karshe sai muka ga yaran da suka zo za su yi zabe kato bayan kato sun fi karfin su iya kula da su su biyu.

“Shi ne muka ce bari mu gyara musu domin kar a samu matsala ko fada ya biyo baya.”

Gardama

“[Samarin] Suna takara tsakanin su biyu… To saboda gudun na hada su rikici sai na ce musu su je su yi zabe, wanda ya fi mutane shi nake so,” budurwar ta shaida wa BBC.

A wani abu mai kama da almara, mutanen gari sun yi zaben fidda gwani tsakanin samarin budurwar a garin Gyade.

Yaran unguwar sun yi zaben ‘yar tinke tsakanin masoyan budurwar, wadda ta shaida wa BBC cewa ta kasa zabar wanda ta fi so ne a cikinsu.

Raba gardama

Ta kuma sanar da masoyan nata cewar jama’ar gari ne za su yanke hukuncin wanda zai aure ta ta hanyar zabe.

Sannan ta bukaci saurayin ya ki janyewa da ya zo da mutanen da ke goyon bayan ta aure shi su jefa masa kuri’a; ita kuma wanda ya fi yawan kuri’u shi za ta so.

“Ni a cikinsu kowa duka ina son sa. Saboda gudun kar wani ya ce na yaudare shi shi ya sa na ce su je su yi kuri’a a kan idon mutane,” in ji ta.

“Kowa ya tabbatar, mutane su zamar mani alkalai. shi ya sa na ce su je su yi zabe.”

Yakin neman zabe

Bayan amincewar samarin da bukatar masoyiyiyar tasu sai abin ya rikide ya koma tamkar yadda aka saba gani a lokacin siyasa.

Kowanne daga cikin samarin biyu ya rika shiga lungu da sako yana bai wa mutane baki su fito su goyi bayansa ranar fidda gwani.

Wani dan uwan budurwar mai suna Aliyu Abdullahi ya ce: “Da saninmu aka yi, har ga Allah. Amma mu da mun dauka kamar abin wasa ne irin na yarinta.

“To daga baya har ga Allah sai muka ga abu ya koma gaske – wasa-wasa gaske-gaske. Sai da aka tara jama’a, dubban jama’a a kan wannan abu.

“Suka zo suna bi gida-gida suna neman goyon bayan mutane su fito su zabe su, wai za su kara a tsakaninsu.

“Har ga Allah mu mun dauki abun wasa ne. To daga baya kuma ga shi abu ya zame gaske.”

A nasu bangaren, mutanen gari kuma suka kafa kwamitin da zai gudanar tare da lura da zaben.

Yadda aka yi zaben

“Jami’an tsaro sun zo wurin; irinsu Civil Defence da Zabgai Security da ‘yan banga…an yi zabe an tashi lafiya an ba da tsaro, goyon baya 100%, aka yi zabe kuma aka tashi lafiya ba a samu wata hayaniya ba,” a cewar Aliyu.

Baturen zaben ya bayyana wa BBC cewa yaran da suka zo wurin zaben sun kusa 600.

“To amma har ga Allah manyan gari ba su san da wannan zabe ba. Ba mu sanar da su lokacin da za a yi zabe b,” kamar yadda Aliyu ya yi karin haske.

Aliyu ya kara da cewa: “Jami’an tsaro sun zo wurin; irinsu Civil Defence da Zabgai Security da ‘yan banga.

Sakamakon zabe

Baturen zaben, Umar Saleh ya ce wanda ya ci zaben ya samu kuri’a 331 yayin da abokinsa ya samu kuri’a 211.

“Ka ga kuri’un da aka kada a wurin 542 ke nan.”

Umar ya ce da da farko samarin sun yi na’am da sakamakon zaben amma daga bisani wanda aka kayar ya yi watsi da zaben kuma ya ce zai kai kara gaban kotu.

“Da ma tsarin da muka yi akwai kotunmu muka tanada.”

Bayan wanda aka kayar ya kai kara kotun, ya kuma kai maganar gaban hakimi.

“Sakamakon hakimin ba ya gari shi ne ya ce a bari sai ya dawo, shi ne zai kira mu a tattauna a ga ya za a yi. In sakewa ne ma za a sake.”

Shin za a bai wa wanda ya yi nasara auren budurwar? Tambayar da BBC ta yi wa ‘yan uwanta ke nan.

Maganar aure

Yayan budurwar ya ce suna jiran sakamakon zaben kuma da zarar an kawo shi ba za ta kara kula wani ba sai wanda ya yi nasara.

To ko yaushe hakan za ta faru?

“Maganar aure kuma, idan iyayen yaro suka kawo tambaya, ko gobe za mu bari su ci gaba da kula juna. Za mu bari ya aure ta.”

Dangin budurwar

Da take magana game da tambayar da BBC ta yi mata ko shin da sanin iyayenta aka yi zaben, budurwar ta ce: “Da sa hannunsu kuma da bakinsu a ciki. Sun amince, suka ce a je a buga zaben.”

Yayanta Aliyu Abdullahi ya ce: “Da saninmu aka yi, har ga Allah. Amma mu da mun dauki abin wasa ne irin na yarinta.

Dangin saurayi

Amma Malam Danladi Ibrahim, kawun saurayin da ya yi nasara a zaben ya ce wasa ne kawai aka yi tsakanin yara kuma aka yada a shafukan zumanta, amma dansa bai isa aure ba.

More from this stream

Recomended