Zaben Amurka na 2020: Shin masu fafutukar Black Lives Matter za su iya tasiri a zaben kasar?

Masu fafutukar kare hakkin bakaken fata da ake yi wa lakabi da Black Lives Matter sun kwashe tsawon lokaci suna hankoron ganin an kare martabar bakar fata a Amurka.

Fafutukarsu ta samu karbuwa sosai bayan kisan da ‘yan sandan kasar suka yi wa wani bakar fata da baya dauke da makami, Mr George Floyd.

Hakan ya harzuka mutane da dama a kasashen duniya inda aka rika gudanar da jerin gangami a birane daban-daban na duniya.

Sai dai wasu ‘yan siyasa irin su Shugaba Donald Trump sun bayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta’adda.

Amma duk da haka wasu da ke fafutuka cikin ta sun tsaya zabuka kuma sun yi nasara.

Shin wannan fafutuka za ta iya yin tasiri a kan sakamakkon zaben kasar na 2020?

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...