Mataimakin shugaban ƙungiyar Hezbollah ya yi fatal da kiraye-kirayen da ake masu na kada su shiga yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Gaza da Isra’ila.
A cewar Na’im Qassem, ƙungiyarsu a shirye take don yaƙar Isra’ila idan akwai bukatar hakan.
Ko satin da ya gabata ƙungiyar Hezbollah ta gwabza rikici da dakarun Isra’ila a kan iyakar Labanon.
Kalaman na ƙungiyar sun zo daidai lokacin da ministan harkokin wajen Iran ya kai ziyara a birnin Beirut.
Tehran na ba da tallafin kuɗi da na soji ga Hizbullah.