Za mu sake duba shirin tallafin N8000 ga ƴan Najeriya

A wani al’amari na baya-bayan nan, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana sake fasalin shirin farko na raba tallafin kudi na Naira 8,000 ga gidaje miliyan 12 duk wata na tsawon watanni shida.

Matakin dai ya zo ne a matsayin mayar da martani ga sukar jama’a da damuwar da kungiyoyin kwadago suka yi, wadanda ke ganin cewa shirin ya gaza wajen rage wahalhalun da ke tattare da cire tallafin man fetur.

Da yammacin ranar Talata, wata sanarwa da Dele Alake, mai baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa, da dabaru ya fitar, ta mika umarnin shugaban kasa na sake duba shirin mika kudi naira 8,000 da aka kayyade da nufin samar da agaji ga gidaje masu rauni.

Tinubu ya ba da umarnin cewa a gaggauta bayyana dukkanin matakan da gwamnati ta dauka na rage wa al’ummar Najeriya wahala.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...