Connect with us

Hausa

Za mu dauki mataki kan jifar shugabanninmu a Ogun – APC

Shugaba Muhammadu Buhari

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan yadda aka jefi shugabanninta a gangamin yakin neman zaben shugaba Buhari a jihar Ogun.

Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta ce za ta dauki mataki kan gwamnan jihar Ibikunle Amosun wanda ta zarga da shirya cin mutuncin ga shugabanta Adams Oshiomhole a gaban idon shugaba Buhari.

A ranar Litinin ne wasu suka jefi Adams Oshiomhole a yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke gangamin zabensa a birnin Abeokuta.

An jefi Oshiomhole ne bayan da ya ambaci sunan dan takarar gwamna na APC a jihar, Mista Dapo Abiodun wanda gwamnan jihar ba ya goyon baya, matakin da ya harzuka mutanen da suka halarci gangamin.

APC ta ce ba za ta lamunce wa wannan rashin da’a ba daga duk wani mambanta.

Ta ce za ta yi nazari kan abin da ya faru inda aka kunyata Buhari da shugabanninta kuma za ta dauki mataki akai bayan an kammala zabe.

Lamarin ya kai sai da jam’ian tsaro suka rika kare shugaba Buharir daga masu jifa kafin kammala taron.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Grrrrrr! Ashe yin fushi ma abu ne mai kyau?|BBC Hausa

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mafi yawan sassan fadin duniyarmu ana zaune ne cikin lumanar zaman lafiya da wadata.

Kididdigar alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasuwanci ta duniya da gwamnatoci daban-daban a fadin duniya suka tattara sun nuna cewa kasashe da dama talauci na raguwa, sannan tsawon rai na karuwa.

Mafi yawan wadanda ke zaune a kasashen da suka ci gaba suna da kariya, kuma sun samu karuwar dukiya fiye da kowane zamani a tarihin dan Adam.

Shin wane dalili ne ya sanya mutane da yawa ke yin fushi a kodayaushe?

Akwai labaran fusata a kan titi, zazzafar takaddamar kafofin sada zumuntar intanet, a wasu lokutan har ‘yan siyasa ke bai wa hammata iska (naushin dambacewa ko kokowa).. a iya yi wa mutum uzuri in har ya dauka cewa duniya ta harzuka da fushi.

Oliver Burkeman – dan jaridar Birtaniya kuma marubucin da ya yi rubutu kan yadda za a samu farin ciki – ya shirya shirin sauya salo, don bin kadin fushi dangane da yadda za a kawo sauyi.

Shin mene ne ke fusata mu? Mene ne ke tunzura lamarin? Ta yiwu mafi muhimmanci shi ne, mummunan abu?

1. Mene ne dalilin harzukar fusatarmu?

An angry man at the wheel of his car

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mene ne ke sanyawa a rika bijirowa ko harzuko mana fushi tun a zamanin da, har ta kai ga wani na jin haushin wani har ya fusata?

“Bacin ran da ke harzuka fushi cukurkudadden al’amari ne mai wuyar sha’ani,” in ji Aaron Sell, Farfesan nazarin kwakwalwa da nazirin miyagun laifuka a Jami’ar Heidelberg a Ohio, da ke kasar Amurka.

“Don fito da lamarin karara, a iya cewa shi ne linzamin zuciya. Wata hanya ta kutsawa cikin tunanin wani, ta yadda za ka sanya ya kimantaka da daraja. Wata hanya ce ta samun nasarar rikicin da ke tsakaninku, tare da sauya masu tunanin.”

Farfesa Sell ya kwatanta yadda muhimmin bangaren “linzamin tunanin zuci” ke bijirowa daga “fuskantar fushi ya kambama tayar da jijiyoyi da hucin hura hanci.”

“Kowane daya daga wadannan sauye-sauyen da fushi ke haifarwa a fuska na fito da alamun karfinka/ki da jarumta a zahiri.”

A cewar Farfesa Sell, masana kimiyya sun samu kai ga gacin fahimtar cewa ” fushin fuska” gadonsa ake yi ba koya ake yi ba, saboda “yara makafi suna bijiro da yanayin fushi da aka saba gani a fuskokinsu.”

To ta yaya kyakkyawan “fushin fuska” ya haifar wa magabatanmu nasara (samun rinjaye kan al’amuran rayuwa?

Presentational grey line

2. Mahangar “sake salon gyaran tarairayar al’amura”

A variety of people from all over the world, all with angry faces

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ta yiwu ka ji cewa magabatanmu (kakanin kakanninmu) wadanda ba sa bata rai (yin fushi) har su yi fada sun yi nisan kwana fiye da wadanda suka yi (fushi), amma dai ba haka lamarin ya kasance ba.

“Abin da ya faru, a cewar Farfesa Sell, shi ne, “mutanen da suka damfaru da wani nau’in bacin rai da ke bijiro da fushi sun fi saurin harzukar fusata fiye da wadanda ba sa yi.”

Sun yi hakan ne ta hanyar saukaka daidaituwar kyawawan al’amura, har ta kai ga sun yi galaba wajen takaddamar rashin fahimta (ko jayayyar son rai – fifikon ra’ayi)

“A da, mutane wadanda ba sa nuna bacin rai ko fushi a kan tumurmusa su a tauye,” in ji Farfesa Sell, wato mutane kan yi musu sata, sannan su wulakanta su, sakamakon haka “sai a kawar da su ko ma a daina jin duriyarsu, sun bata bat.”

Wadanda suka tsira su ne wadanda suka yi barazanar janyewa daga hadin gwiwar taimakekeniya (a junansu), inda nan take sukan tunatar da daukacin kyawawan abubuwan da suka aikata, ta yadda sukan sanya mutum dan uwansu ya dawo da baya ya yi ta yaba musu – lamarin da ke haifar da kyakkyawar tarairaya (a tsakanin juna).

Bacin ran nuna fushi shi ya fifita irin wadannan mutane da fifikon bunkasar rayuwa, a cewar Farfesa Sell.

3. Mene ne ke faruwa da jikinmu da zarar mun yi fushi?

Two schoolgirls having a fight at playtime

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Don fahimtar fushi muna bukatar yin tunani kan tasirinsa ga jikinmu a zahirance, ta yaya yake zaburar da mu ko kai tsaye yaya tunaninmu ke gushewa.

Farfesa Ryan Martin kwararen mai nazarin lafiyar kwakwalwa a Jami’ar Wisconsin-Green Bay ta Amurka mai bincike ne da ke bibiyar abin da ya danganci fushi, yana gudanar da shirin bin kadin daukacin harzukar fushi na “All the Rage” da ake watsawa ta wani salon sakon rediyon podcast a kowane wata.

“Da zarar kun yi fushi, tsarin sadarwar jijiyoyinku da ke tausasa tarairayar fafata fadanku ko yunkurin fafatawa sai su zabura su fara aiki,” a cewar Farfesa Martin, “Bugawar zuciya sai ya karu, numfashinku ya karu, sai ku fara zufa, kuma tsarin sarrafa abincin ku ya rinka tafiya a hankali.”

Wannan yamutsin martanin da kwakwalwa ke yi, mataki ne da jiki ke dauka da manufar nuna karfin tunkarar kowane irin rashin adalci da kuke jin an yi maku.

Ita ma kwakalwa na aiwatar da ayyukan ne daki-daki.

“Mun kuma san cewa duk sa’adda mutane suka harzuka da gaske, to tunaninsu zai bijiro a hankali ya rika gudanar da ayyuka daki-daki,” a cewar Farfesa Martin, “Sun fi zaburar dabarun tsira” ko “na daukar fansa.”

Wannan lamari ne da ke bunkasa shi ma dai ba ku yin tunani kan sauran al’amura lokacin da kuke kokarin daukar mataki kan wani abin da kuke jin ba a kyauta maku ba (an yi ba daidai ba, ko rashin adalci).

Presentational grey line

4. Mene ne ya sanya rayuwar zamani ke harzuko mana fushi?

Angry man on the phone

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Akwai tabbacin cewa, mafi yawan mutane, musamman wadanda ke zaune a kasashen da suka ci gaba damuwarsu kadan ce in an kwatanta da magabatansu (kakannin kakanninsu), shi ya sa ake bin bahasin dalilin da ya sanya rayuwar wannan zamanin take cike da harzukar bacin rai da ke tunzura fushi?

Lamarin na da saukin fahimta, a cewar Farfesa Martin: “Mutane al’amura sun sha musu kai, ta yadda suna da dimbin bukatun rayuwa, don haka sakamakon kakarewar harkoki sai a ji matukar rashin dadi.”

Saukin lamarin shi ne, a cewar Farfesa Martin: “Al’amura sun sha wa mutan kai ga bukatun rayuwa na karuwa, to sakamakon hakan da mutum ya ji harka ta tsaya cik to al’amura ke nan sun yi matukar muni (a rayuwa).”

Idan ya zama dole mu bi layi a katafaren shagon sayar da kayayyaki ko mun samu tsaiko daga mai kawo mana makamashi, sai kawai mu harzuka da fushi saboda ba mu da lokacin da za mu bata.

Wannan shi ne abin da ya kamata a ce “an kauce masa, tattare da jin cewa ba a iya tabuka komai” al’amarin da ke sanya harzukar fushi (na nuna rashin jin dadi), a cewar Farfesa Martin.

Su ne al’amuran da “ya kamata a kauce musu, don sukan jefa mu cikin halin rashin iya yin katabus” har mu fusata, a cewar Farfsa Martin.

Yadda bacin rai ke bijiro mana da fushi tattare da irin matakin da muke dauka “ba a kodayaushe lamarin ke da alfanu a duniyarmu ta wannan zamanin.”

Presentational grey line

5. Za mu iya shawo kan fushinmu fiye da yadda muke tsammani?

Pop art style illustration - a woman imagining swear words, represented by symbols

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hakika cutar da mutumin da kuke ke fushi da shi ba abu ne mai alfanu ba – don haka akwai bukatar mu san yadda za mu tarairayi fushinmu.

Muna iya shawo kan lamarin fiye da yadda muke zato, a cewar Maya Tamir, Farfesan nazarin kwakwalwa a Jami’ar Hebrew ta Jerusalem.

Sosuwar zukata ba shi da fa’ida tun da bunkasar harzuka yake haifarwa, a cewar Maya, “al’amura ne da ake samun horo a kai, sai mu sauya, mu tasirantu da dabarun sarrafa juya akalar yanayinmu.”

Bincikenta ya nuna cewa ba kodayaushe ne fushi ke haifar da rikicin fada ba.

“Mu ba ‘yan kore ba ne da ke lilo, inji Maya. “Bacin ran nuna fushi ba ya mayar da mu mafadatan da ba za su iya tarairayar hankalinsu (ko kawunansu ba).”

Presentational grey line

6. Yin kyakkyawan aiki mai amfani lokacin fushi

A small boy - pretending to be a grown-up - working hard at a desk

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Bacin rai dai kan iya matukar harzuka mu (cikin dugunzumar fushi) zai iya tunzuro da fada da zage-zage kai har ma takaddamar fada mai zafi a shafin Twitter.

Idan wadanda ke bukatar ganin sun kankane karfin ikonsu da matsayinu suka yi fushi, sakamakon hakan na iya haifar da mummunan al’amari – ko ma a karshe da yaki.

Amma masanan fannin kula da kwakwalwa sun ce zai iya tunkarar tunaninmu, ya kara masa karsashin zaburarwa don daukar mataki lokacin da aka aikata mana ba daidai ba.

Mark Vernon , masanin falsafa (kula da juya akalar tunani) da kula da lafiyar kakwalwa, ya bayyana yadda mutanen da, na zamanin Plato da Aristotle (masanan alkiblar juya akalar tunani) suke da tabbacin cewa akwai abin da ake yi wa lakabi da “fushi mai kyau.”

Sai su ji cewa wanda ke cikin fushi zai yi kyau garesu idan lokacin da suke fushin sun sarayar da harzukar fushinsu wajen gudanar da kwakkwaran aiki (mai amfani).

Saboda haka, harzukar fushi dai “tana iya zabuar da mutum ya aikata wani abu gaba-gadi (da kwarin gwiwa kai tsaye) ko ta zaburar da su yi muhawara mai kyau da za ta bayar da damar warwarewa ko shawo kan takaddamar cikin adalci.

Don haka an gano shi cewa: ba za a iya cewa daukacin fushi ba shi da fa’ida.

Kawai abin da muke bukata shi ne tarairayar juya akalar wannan kakkarfan lamari, mai matukar sosa zuciya, ta yadda za a sarayar da shi da kyakkyawan tasiri, don gudun ka da mu karasa da dabaibayin bacin rai da zakuwar kai farmakin fada.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Everton ta lallasa Man United

Premier

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Manchester United ta debi kashinta a hannu bayan Everton lallasa ta 4-0 a wasan mako na 35 a Premier da suka fafata ranar Lahadi a Goodison Park.

Everton ta ci kwallo biyu tun kan aje hutun rabin lokaci ta hannun Richarlison de Andrade da kuma Idrissa Gueye.

Bayan da suka koma zagaye na biyu aka kara zura kwallo biyu a ragar United ta hannun Lucas Digne da kuma Theo Walcott.

United, wadda ta buga karawar kamar ‘yan wasanta ba su da lafiya ta samu dama daya kacal da ta buga kwallo ta nufi raga saura minti hutu a tashi daga fafatawar.

Marcus Rashford ne ya samu damar a cikin masu tsaron bayan Evrton, ya kuma buga kwallo ta wuce saman kan mai tsaron raga Jordan Pickford.

Wannan nasarar ta kai Everton zuwa mataki na bakwai a teburin Premier, hakan zai iya kai ta gasar Europa a badi, ita kuwa United ta ci gaba da zama a matakinta na shida.

Sauran maki biyu ne tsakanin United da Arsenal ta biyar a teburi, wadda za ta fafata da Crystal Palace ranar Lahadi.

A ranar Talata ne Barcelona ta fitar da Manchester United daga gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana, kuma ba ta kai bantenta a FA Cup ba, kuma Manchester City ce ta lashe Caraboa Cup na shekarar nan.

Everton ta taba cin United 3-0 a gasar Premier ranar Lahadi 26 ga watan Afirilun 2015 a Goodison Park.

Yadda kungiyoyin suka murza-leda.

Hakkin mallakar hoto
BBC Sport

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Masu zanga-zanga na jiran sanarwar mika mulki ga farar hula a Sudan

Protesters have continued to stage a sit-in in central Khartoum

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Masu zanga-zanga a kasar Sudan na kokarin sanar da majalisar da farar hula za ta jagoranta da suke so ta jagoranci kasar wace za ta kasance a matsayin gwamamnatin rikon kwarya bayan hambarar da Omar al-Bashir.

Dubban masu zanga-zangar na ci gaba da haduwa a wajen shelkwatar rundunar sojojin kasar da ke birnin Khartoum.

Shugabannin da ke jagorantar zanga-zangar na ci gaba da tattaunawa da sojojin kasar tun bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.

A ranar Lahadi ne dai sojojin suka bayyana aniyarsu ta ba farar hula mulki, amma suna kokarin kafa majalisar da farar hular za ta jagoranta da taimakon sojojin.

Me shugabannin masu zanga-zangar ke shiryawa?

Kungiyar Sudanese Professionals Association (SPA), ita ce kungiyar da ta jagoranci zanga-zangar da ta yi sanadiyar juyin mulkin hambarar da Omar al-Bashir kuma har a yanzu, ita ce gaba-gaba wajen gudanar da zanga-zanga da kuma tattaunawa da sojojin wajen ganin cewa mulki ya dawo ga farar hula.

Tun a baya dai, daya daga cikin jagoran kungiyar ta SPA ya bayyana cewa wannan zai iya kawo tsaiko wajen bayyana majalisar riko ta farar hula amma ya tabbatar da cewa sanarwar za a yi ta ne a ranar Lahadi a filin da ake gudanar da zanga-zangar.

Masu zanga-zangar na san majalisar rikon ta zamana ita ce za ta ci gaba da gudanar da harkokin gwamanti har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe a kasar.

Me sojojin za su yi?

A ranar Lahadi, sojojin sun amsa da cewa za su amsa kiran da masu zanga-zangar suke yi na mulkin farar hula cikin mako daya inda suka bayyana ra’ayinsu na majalisar ta zamana ta hadaka tsakanin farar hula da sojojin.

Tun tuni dai sojojin ke nuna tirjiya wajen mika mulki ga farar hula inda suka ki bayar da kai domin bori ya hau.

Amma kuma sojojin sun saki wasu daga cikin ‘yan siyasar da ke gidan kaso inda kuma a wani bangaren kuma sojojin suka kama wasu daga cikin mukarraban Omar al-Bashir.

Duk da cewa sojojin sun yi alkawarin ba za su kori masu zanga-zangar daga filin da suke gudanar da ita ba, amma sun yi kira garesu da su bari a ci gaba da rayuwa cikin walwala.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: