Za a shata layi tsakanin gwamnatin Kano da Arewa24

Shirin Kwana Cas'in

Bayan dakatar da nuna shirin Kwana Cas’in da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta yi, alamu na nuna gidan talbijin na Arewa24 zai yi biris da matakin.

A ranar Talata ne hukumar tace fina-finai ta jihar Kanon ta fitar da sanarwar dakatar da ci gaba da nuna shirin Kwana Cas’in da shirin Gidan Badamasi wadanda suka yi tasiri sosai ga dimbin masu kallo a sassan duniya.

Shugaban hukumar tace fina-finan na Kano Isma’ila Na’abba Afakallah ya shaida wa BBC cewa fina-finan biyu sun ci karo da tsarin dokokin hukumar, inda ya ce a shirin Kwana Cas’in an nuna maza na cacumar wata yarinya.

A shirin Gidan Badamasi kuma ya ce an yi amfani da kalaman da ba su dace ba, wadanda dukkaninsu a cewar Afakallah sun saba wa sashe na 102 na dokar da ta kafa hukumar tace fina-finai a 2001.

Duk da cewa kafar Arewa 24 ba ta ce komi ba, ko fitar da sanarwa game da matakin dakatar da shirye-shiryenta da aka yi, amma kafar ta wallafa bidiyon dandanon shirin da za a nuna mako na gaba a shafinta na Twitter, kwana guda bayan dakatar da nuna shirin da hukumar tace finafinai ta Kano ta yi.

Wata majiya kuma da ke kusa da shugabannin kafar talabijin ta Arewa24 ta tabbatar da cewa za a ci gaba da fim din, duk da dakatarwar da hukumar tace finafinai ta Kano ta yi.

Shirin Kwana Casa’in wasu kungiyoyin duniya da hadin gwiwar gidauniyar MacAurther ne ke daukar nauyinsa, yayin da kuma Falalu Dorayi ne furodusan shirin Gidan Badamasi.

Afakallah ya ce “Mun dakatar da su ne saboda yadda aka nuna ana cacumar mata wanda ya saba da dokar hukumar tace fina-finai inda aka nuna maza sun kama wata yarinya suna jan jikinta wanda ya saba wa ala’ada.”

“An kuma yi amfani da laffuzzan da ba su dace ba a cikin shirin Gidan Badamasi,” in ji shi.

Labarin dakatar da shirye-shiryen bai yi wa dumbin masu kallo dadi ba, inda ake ganin babu wani shiri da ake yawan kallo da ake nunawa a wata kafar talabijin a arewacin Najeriya kamar sa.

Shirin Kwana Cas’in ya shafi siyasa da kuma bankwado yadda rashawa ta yi katutu a harkokin gwamnati, wani dalilin da wasu ke ganin shi ya sa gwamnatin Kano ta yi amfani da hukumar tace fina-finai aka dakatar da nuna shirin.

Kazalika shirin na nuna irin yadda wasu talakawa suke da hadama da rashin gaskiya a mu’amalarsu ta yau da kullum.

Sharhin Masana

Masana na ganin dakatar da nuna shirye-shiryen guda biyu da hukumomin Kano suka yi yana da alaka da siyasa.

Muhsin Ibrahim, mai nazari kan fina-finan Hausa kuma wanda ke koyarwa a Jamus, ya ce ba yau aka fara laifin da ake tuhumar shirye-shiryen da yi ba.

Ya bayar da misalai inda ya ce: “akwai fitowa da aka samu cudanya tsakanin maza da mata a shirin Dadin Kowa. Hukuma ba ta taba magana ba saboda shirin bai shafi siyasa kai tsaye ba kamar Kwana Casa’in.”

Ya kara da cewa kamata ya yi hukumar tace fina-finai ta bi hanyar lalama kan lamarin, musamman idan Arewa24 ta ci gaba da nuna shirye-shiryenta, wanda kuma har zai kai su zuwa kotu.

“Arewa24 na iya yin galaba a karar, wanda kuma zai iya shata wa hukumar tace fina-fainai iyaka.”

Yanzu dai an jira a gani shi ne ranakun Lahadi da Laraba lokutan da ake nuna shirye-shiryen na Kwana Casa’in da Gidan Badamasi.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...