Za a sa wa masu amfani da shafin Tuwita haraji

Mai kamfanin sadarwa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) Elon Musk ya bayyana cewa akwai yiwuwar duka masu amfani da shafin su rinka biyan wasu ‘yan kudade a duk wata.

Musk ya bayyana haka ne a a ranar Litinin a lokacin da yake tattaunawa da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bayan firaiministan ya yi tambaya kan yadda Musk zai magance yadda ake amfani da shafukan bogi wurin tunzura kiyayyar Yahudawa.

Daga nan ne Musk ya ba shi amsa inda ya ce kamfanin zuwa gaba na son a fara biyan kudade kadan kafin a rinka amfani da shi.

Babban dan kasuwan mamallakin kamfanin SpaceX da Tesla ya gudanar da sauye-sauye da dama tun bayan da ya karbi jagorancin Twitter inda ya sayi kamfanin kan sama da dala biliyan 44 a Oktobar bara.

More News

An samu ambaliyar ruwa a Adamawa

Anguwan Tana, al’ummar karamar hukumar Yola ta Arewa, sun shiga tasgaro a ranar Alhamis sakamakon ambaliya daga kogin Kilange da kogin Faro. Mazaunan garin...

Sojoji sun ceto mutane 6 daga cikin ɗaliban jami’ar Gusau da aka sace

Sojoji sun ceto dalibai mata shida daga cikin daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau da aka bada rahoton yan bindiga sun yi garkuwa da...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau

An sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ba a tantance adadinsu ba da sanyin safiyar Juma’a. ‘Yan ta’addan masu yawan gaske sun...

Ƴan sanda sun kama masu safarar makamai wa ƴan bindiga

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Karasuwa a jihar Yobe sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da...