Za a rataye wanda ya ɗaba wa wani wuƙa har lahira

An yanke wani mutum mai suna Hamza Mohammed  hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da ya daba wa wani mutum wuka har lahira a lokacin wani rikici a jihar Neja.

An ce Mohammed da wani Baba Usman sun bi mamacin mai suna Isah Mohammed har sai da suka kama shi suka yi ta caka masa wuka har ya mutu.

Lamarin dai ya faru ne a shekarar 2015 a yayin wani liyafa inda aka yi wa ‘yan uwa matasa ‘yan bangar siyasa a yankin Kpakungu da ke Minna da kuma matasan Barikin Saleh.

Nan ne aka kashe Isah Mohammed da wuka har lahira.

An fara gurfanar da Mohammed ne a watan Agustan 2015 a hannun wasu jami’an sashen kisan kai na rundunar ‘yan sandan jihar Neja bisa zargin aikata laifuka biyu da suka hada da hadin gwiwa da kuma kisan kai, laifin da ake tuhuma a karkashin sashe na 79 da 221 na kundin laifuffuka.

Related Articles