Za a rantsar da Emmerson Mnangagwa ranar Lahadi

[ad_1]

Magoya bayan shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Magoya bayan shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe

Kotun koli ta Zimbabwe ta tabbatar da nasarar da shugaba Emmerson Mnangagwa ya samu a zaben shugaban kasar da ya gudana.

A dalilin haka za a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasa ranar Lahadi.

Jam’iyya mai adawa da gwamnati ta ki amincewa da sakamakon zaben, kuma ita ce ta shigar da wannan karar.

Mista Mnangagwa ya zama shugaban kasa ne bayan da aka hambare gwamnatin Robert Mugabe wanda ya mulki kasar har na tsawon shekara 37.

Jam’yyar adawa ta Movement for Democratic Change ta bukaci a soke sakamakon zaben ne gaba daya, bayan da ta yi zargin an tafka gagarumin magudi a lokacin zaben.

Amma dukkan alkalai tara na kotun kolin Zimbabwe da suka saurari karar sun ce jagoran MDC Nelson Chamisa ya gaza bayar da kwararran hujjoji na aukuwar magudin zabe.

Alkalin alkalan kasar Luke Malaba ya kuma ce ‘yan adawan ba su iya gamsar da dukkan alkalan cewa jam’iyyar shugaba Mnangagwa ce ta aikata laifukan zaben ba.

Bayan da aka bayyana hukuncin kotun kolin, Mista Mnangagwa ya yi kira ga ‘yan kasar da su rungumi zaman lumana da hadin kai.

Tarayyar Turai ma ta yi kira ga ‘yan kasar da su yi hakuri kuma su guji daukan matakan da ka iya janyo tashin hankali.

Amma duk da Mista Mnangagwa ya yi nasara a zaben, zai taras da manyan matsaloli na jiransa ya warwaresu.

Akwai batun siyasar kasar da ke neman kulawa, da kuma na tattalinarziki da ya riga ya ruguje gaba daya, ban da matsalar gyaran yadda duniya ke kallon kasar a matsayin wadda ta gaza.

[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...