Hukumar EFCC dake yaÆ™i da masu yiwa tattalin arzikin Æ™asa ta’annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta.
A ranar Laraba, Michael Ohiare daraktan ofishin yaÉ—a labarai na tsohon gwamnan ya sanar da cewa Bello ya amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa kan zargin da ake masa na yin almubazzaranci da kuma aikata al-mundahanar kuÉ—aÉ—en da yawansu ya kai biliyan 82.
Michael ya ce Bello ya É—auki wannan matakin ne bayan da ya tattauna da iyalansa, abokanan siyasarsa da kuma tawagar lauyoyinsa.
Amma a wata sanarwa da hukumar ta fitar, Dele Oyewale mai magana da yawun EFCC ya ce har yanzu suna neman Yahaya Bello ruwa a jallo.
Oyewale ya ce maganganun da ake yaÉ—awa cewa Bello yana tsare a hannunsu ba gaskiya ba ne.
A ranar 18 ga watan Afrilu ne hukumar ta EFCC ta ayyana Bello a matsayin wanda ta ke nema ruwa-a-jallo bayan da ƙoƙarin kama shi ya gaza samun nasara.