AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai.

A taron da aka yi a ranar Talata a Sokoto wanda gidauniyar Attahiru Bafarawa ta shirya, Bafarawa ya ce tallafin yana nuna godiya ga amincewar da al’ummar jihar Sakkwato suka yi masa ta hanyar zabarsa a matsayin gwamnansu na tsawon shekaru takwas. 

Ya ce abin bai wa jama’a kyauta ne, ya kara da cewa babu sauran lokacin da za a mayar wa jama’a kamar yanzu yunwa da wahalhalun da ake ta fama da su a kasa.

Ya ce lokaci ne da ya kamata a mayar da hankali, yana mai cewa.

More from this stream

Recomended