Za a hukunta waɗanda ke da alhakin kai harin bam a ƙauyen Kaduna

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce wadanda suka kai harin bam da jirage marasa matuka a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna ba za su sha ba.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a lokacin da ya ziyarci Kaduna domin jajanta wa gwamnatin jihar kan harin bam da aka samu bisa kuskure wanda ya faru ranar Lahadi.

Mataimakin shugaban kasan ya kuma ziyarci asibitin kwararru na Barau Dikko da ke Kaduna, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a lokacin da lamarin ya faru.

A cewarsa, gwamnatin tarayya za ta kuma samar da dukkanin ababen more rayuwa da suka hada da makarantu da asibitoci.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...