Za a hukunta Abdulsalam da Tawakkaltu kan nuna rashin ɗa’a

Wasu dalibai biyu na kwalejin ilimi ta jihar Kwara dake Ilorin za su fuskanci kwamitin ladabatarwa kan zargin da ake musu na nuna rashin ɗa’a a yayin bikin kammala karatunsu.

Daliban da abun ya shafa sun haɗa da Sulyman Tawakkaltu da Muhammad AbdulSalam dukkansu na sashen karatun aikin noma.

A wani hoto da ya karaɗen kafar sadarwar zamani ya nuna Abdulsalam riƙe da nonon Tawakkaltu a yayin bikin kammala karatunsu.

A cewar wata takarda da makarantar ta fitar za a hukunta daliban ne kan yadda suka nuna rashin ɗa’a.

Makarantar ta umarci kwamitinta na hukunta daliɓai da su ɗauki matakin kan daliban biyu domin ya zama izina ga sauran ɗalibai.

More from this stream

Recomended