Za a fuskanci daukewar wutar lantarki a jihohin Filato, Gombe da Bauchi

Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Jos(JED) ya ce al’ummar jihohin Bauchi, Plateau da kuma Gombe za su fuskanci daukewar wutar lantarki daga ranar 28 ga watan Agusta ya zuwa ranar 2 ga watan Satumba.

A cikin wata sanarwa ranar Juma’a mai magana da yawun kamfanin, Friday Elijah ya ce za a samu daukewar wutar lantarki daga karfe 09:00 na safe zuwa karfe 05:00 na yammacin kowace rana a tsawon kwanakin.

Shirin na dauke wutar lantarki da kamfanin Rarraba Hasken Lantarki na kasa TCN ya shirya yi zai bawa ma’aikatan kamfanin damar saka wasu na’urori.

Elijah ya shawarci abokan huldar kamfanin da suyi hakuri da halin da ake ciki inda ya kamfanin ya ci alwashin inganta ayyukansa.

More from this stream

Recomended